Gwamnatin tarayya ta cigaba da dokar hana taron jama’a.

Kwamitin (PSC) kan COVID-19 a ranar Litinin ya ce dokar hana taron jama’a ta kasance yayin da take sanar da kashi na hudu na sassaucin takunkumin COVID-19.

 Kwamitin ya kuma ce cibiyoyin taron, wuraren shan giya, wuraren kulawar dare, za su kasance a rufe har sai sanarwa ta gaba.

Shugaban Technical Sakatariat Mukhtar Mohammed, wanda ke magana a taron PSC kan COVID-19, ya ce takunkumin ya fara aiki daga Talata, 11 ga Mayu 2021.
 

Mohammed ya ce an iyakance taron jama’a zuwa mutane hamsin kuma dole ne su bi matakan nisanta jiki da sauran ka’idoji na kariya.
 

Ya kara da cewa duk wasu wuraren shakatawa, wuraren motsa jiki da sauransu duk zasu kasance a rufe har zuwa ranar sha daya ga watan Yuni lokacin da za a sake duba halin da ake ciki.
 

Ya kara da cewa, “Za mu ci gaba da kiyaye doka kan dawo da aikin ma’aikatan gwamnati daga Mataki na 12 da kasa.  Hakanan za mu takaita tarurrukan gwamnati zuwa dandamali na zamani kamar yadda ya kamata. ”

 “Yakamata makarantu suyi la’akari da amfani da kayan gwajin domin tabbatar da lafiyan jiki.

Mohammed ya ci gaba da sanar da cewa za a sanya dokar hana fitar dare a duk fadin kasar daga karfe sha biyu na safe zuwa karfe hudu safe, sai dai ga masu gudanar da ayyuka na musamman da fasinjojin kasashen duniya, wadanda suka shigo kasar ko kuma suka fita daga kasar.
 

Ya kira dukkan hukumomin tsaro da su aiwatar da wadannan tsare-tsaren sannan kuma ya yi kira ga gwamnatocin jihohi da su hukunta masu karya doka.

 “Wadannan matakan anyi su ne don baiwa gwamnatin Najeriya damar yaki da wannan annoba yadda ya kamata tare da ci gaba da karfafawa da kare rayukan ‘yan Najeriya da tattalin arzikin mu”, in ji Mohammed.

Maryam Gidado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *