Gwamnatin Tarayya ta hana matafiya daga Brazil, Indiya, Turkiyya shigowa saboda karuwar cutar COVID-19,

Kwamitin PSC tayi magana kan COVID-19 inda take cewa matafiya da suka ziyarci Brazil, Indiya ko Turkiyya a cikin kwanaki goma sha hudu za a hana su shiga kasar Nijeriya daga Talata, hudu ga Mayu 2021.

Kwamitin ya ce haramcin ya kasance sakamakon karuwar  cutar ta COVID-19 a kasashe da dama musamman a kasashen da abin ya shafa wadanda suka yi kamari da yawan mace mace

Boss Mustapha, Sakataren Gwamnatin Tarayya daShugaban kwamitin PSC na COVID-19, a cikin wata sanarwa ya yi gargadin cewa kamfanonin jiragen sama za su biya tarar dala dubu uku da dari biyar ga duk wani fasinja da ya shigo kasar

Mustapha ya ci gaba da sanar da cewa ‘yan Nijeriya da wadanda ke da izinin zama na dindindin daga wadannan kasashen za su yi kwanaki 7 na killace su a wani wurin da gwamnati ta amince da shi.

Shugaban ya kara da cewa Fasinjoji (jiragen) da ke shigowa Najeriya daga wasu wurare Dole ne a keɓance su, keɓancewa na kwanaki bakwai sannan a gudanar da gwajin COVID-19 PCR a rana ta bakwai din a ɗakunan binciken da aka zaɓa;  kuma a sa ido don bin ka’idojin keɓewa daga hukumomin da suka dace.
Shugaban ya ci gaba da sanar da cewa, an rage lokacin da za a fara gwajin COVID-19 PCR ga dukkan fasinjojin da ke zuwa Najeriya daga awa tis’in da shida zuwa awa saba’in da hudu

“Daga yanzu ba za a kuma karbar sakamakon gwajin PCR da ya girmi awa saba’in da biyu kafin tashi ba”, in ji shi.
Ya kuma bukaci yan Najeriya da su guji duk wata tafiye-tafiye na kasa da kasa zuwa kowace kasa a wannan lokacin kuma musamman ga kasashen da ke nuna karuwar masu kamuwa da cutar.

Mustapha Ya yi kira ga gwamnatocin jihohi da su tabbatar da cewa an sa ido kan dukkan matafiyan da suka dawo daga dukkan kasashen don tabbatar da bin ka’ida na tsawon kwanaki bakwai na kebewar kai da sake maimaita gwajin COVID-19 PCR a rana ta bakwai bayan isowarsu.

Maryam Gidao

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *