Gwamnatin tarayya ta zargi twitter da taimakawa ƴan Biafra

Muna Zargin Shafin Twitter Da Taimakawa Ƴan Biafra- In ji Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin tarayya ta zargi shafin sada zumuntar twitter da taimakawa ƴan Biafra, biyo bayan goge maganar da shugaba Muhammadu Buhari da shafin ya yi a ranar Laraba

Buhari ya wallafa cewar “Matasan da su ke tada ƙayar a yanzu ba su san irin asarar rayukan da aka samu ba a loƙacin yaƙin basasar Najeriya, mu da muka kwashe shekaru 30 a filin yaƙi za mu bi da su ta hanyar da za su fi fahimta”

Bayan ƙorafe-ƙorafe, kamfanin twitter ya goge rubutun , a inda ya ce ” Rubutu ne na cin zarafin bil’adama wanda ya saɓa dokokin kamfanin twitter”

Ministan yaɗa labarai da al’adu Alhaji Lai Mohammaed a loƙacin daya ke maida martani ya zargi twitter bisa ɗaukar wannan matakin

Lai Mohammed ya bayyana yadda kamfanin twitter ya yi shagulatin ɓangaro da irin rubuce-rubucen da yaran Nmandi Kanu su ke yi, shugaban masu ƙoƙarin kafa ƙasar Biafra.

Ya ce ” Kamfanin twitter ya yi burus da rubuce-rubucen da mutanen Nmandi Kanu su ka yi wanda hakan ya ƙarfafa musu gwiwa wajan kashe jami’an ƴan sanda a loƙacin zanga-zangar ENDSARS, sannan da ƙona kayayyakin gwamnati dana ɗaiɗaikun mutane da a loƙacin zanga-zangar”.

Ya ƙara cewa “kamfanin twitter yana da dokokinsa na kansa, waɗanda bana ƙasashen duniya ba ne, Haka zalika, kowanne shugaban ƙasa yana ƴancin ya fito ya bayyana ra’ayinsa dangane da wani al’amari marar daɗi daya ke faruwa a ƙasarsa”.

Daga Mutawakkil Gambo Doko

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *