Gwamnatin tarayya zata Samar da ayyukanyi Ga Milyan biyar Zuwa Milyan goma ga ‘yan Nageriya Inji Ministan Noma Nanono

Gwamnatin Tarayya za ta kirkiro da ayyukan yi kimanin miliyan biyar zuwa 10 a bangaren noma ta hanyar Noma don Abinci da Tsarin Ayyuka, AFJP. Muhammad Nanono, Ministan Noma da Raya Karkara, ya fadi hakan ne a ranar Talata a Abuja a wani taron manema labarai da ya gabatar gabanin bikin ranar Abincin Duniya ta 2020. Ana bikin ranar abinci ta duniya kowace shekara a ranar 16 ga watan Oktoba a kasashe sama da 150 domin wayar da kan duniya game da al’amuran talauci da yunwa. Taken wannan shekarar shine “Shuka, Ciyarwa, Ci gaba

Ministan ya ce, AFJP, wani bangare ne na shirin Shugaba Muhammadu Buhari na Dorewar Tattalin Arzikin Nijeriya, NESP, an kaddamar da shi ne a watan Yulin da ya gabata don samar da karin fili a kowace jiha da kuma samar da rancen kudin ruwa ga manoma, da sauransu. “Kashi na farko na shirin ya samar da sama da mutum miliyan 1.1 da ke cin gajiyar shirin a duk fadin jihohin da kuma FCT. Daga cikin mutane miliyan 5 da za su ci gajiyar shirin na AFJP, Ma’aikatar Aikin Gona ta Tarayya da Raya Karkara ta baiwa manoma 1,138,000 masu cin gajiyar noma a fadin jihohi 36 da kuma FCT a kashi na farkon aiwatarwa. Tun daga farkon noman rani na 2020, Ma’aikatar ta rarraba kayan aiki a
a duk fadin kasar don bunkasa noman abinci.

Nijeriya a shekarar da ta gabata (2019) ta sami ci gaba a fannin noman albarkatun gona. “A cewar bayanan daga Ma’aikatar, noman masara da shinkafa ya tashi daga 12.8 da 12.3 zuwa 13.94 da 14.28 metric tonnes (MMT) bi da bi a bara,” in ji shi. Ministan ya ce, wannan gwamnati ba za ga huta ba face saita magance matsalar Noma Nageriya ta hanyar samar da ingantaccen kayan aikin gona da inganta Tallafi da bunkasa rayuwa (APPEALS) ta ware Naira biliyan 600 a matsayin tallafin rance ga manoma a duk fadin kasar nan. “A kalla manoma miliyan 2.4 ne ake sa ran za su ci gajiyar rancen wanda bashi da riba,” in ji shi. Ya ce wannan karamcin zai tallafawa manoma a kasar nan don inganta kayan aikinsu da nufin bunkasa bangaren noma na kasar.

Tallafin ya kasance ne don tallafawa manufofin Gwamnatin Tarayya kan harkar noma, wanda ya hada da inganta samar da abinci, inganta noman manoma da kuma kara fitar da kayayyaki,” in ji shi. Game da ambaliyar kwanan nan, Ministan ya ce kimanin Jihohi 12 ne abin ya shafa, yana mai cewa wadanda abin ya fi shafa su ne Kebbi da Jigawa wadanda sune manyan jihohin da ke samar da shinkafa. Ya ce barnar da aka yi a Jigawa ba ta kai ta Kebbi ba ” Ministan ya ce gwamnatin tarayya za ta tabbatar an tallafawa manoman rani domin rage tasirin ambaliyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published.