Labarai

Gwanin sha’awa: Gwamna Yahaya bello zai rabawa musilman nageriya littafin Tafsirin Al-Qur’ani na Sheikh Sani rijiyar lemo.

Spread the love

Gwamnan jihar Kogi Alhaji Yahaya Bello ya mallaki Littafin Tafsirin Al-Qur’ani Maigirma fassaran Hausa wanda babban Malamin Hadisin Ash-sheikh Dr Muhammad Sani Umar Rijiyar Ilmi ya rubuta.

Kamar yadda zaku gani a hoto, ga dan uwa babban Alaramma Shattiman Alarammomin Nigeria Alaramma Ismail Maiduguri da Alaramma Saifullahi Umar lokacin da suke mikawa Gwamnan Littafin.

Abin sha’awa da burgewa, Maigirma Gwamna Yahaya Bello ya bada umarni a sayi dubbanin kwafi na Littafin a rabawa al’ummar Musulmi kyauta, hakan ke kara tabbacin da nake kokarin samu cewa Gwamnan ma’abocin addini ne.

Littafin mujalladi shida ne, kuma kudinsa a kasuwa Naira dubu 20, ban san yadda tsarin raba Littafin zai kasance ba, amma idan lokaci yayi zamu sanar a nan domin ‘yan uwa su sami Littafin kyauta daga Maigirma Gwamna.

Muna rokon Allah Ya shiga cikin lamarin Gwamna Yahya Bello, Allah Ya cika masa dukkan burinsa na alheri ga addini da Kasarmu Nijeriya.

Daga shafin Datti Assalafiy

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button