Halinda da Nageriya take Ciki na aminta Cewa Buhari bashi Iya yin Bacci ~inji Jonathan.

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya bukaci Shugaba Muhammadu Buhari da ya hada kai da gwamnoni, shugabannin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki don magance rikicin da ke faruwa sakamakon yawan rashin tsaro a kasar.

Jonathan ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya jagoranci wata tawagar ’yan siyasa daga Bayelsa a ziyarar ta’aziyya da suka kai wa Gwamna Ifeanyi Okowa a gidan Gwamnati da ke garin Asaba na Jihar Delta, sakamakon rasuwar mahaifin gwamnan, Sir Okorie Okowa.
Ya ce abin takaici ne yadda ake sace yaran makaranta da ‘yan Najeriya da dama don neman kudin fansa.

“Na yi imanin cewa tare da jajircewar gwamnoni da Gwamnatin Tarayya, za mu iya magance matsalar rashin tsaro a kasar.

“Na yi imanin cewa Shugaban kasa da kansa ba ya barci kuma gwamnoni ba sa barci kuma game da kalubalen rashin tsaro a kasar.

“Muddin gwamnoni, Shugaban kasa da dukkan hukumomin tsaro za su iya aiki tare, Najeriya za ta iya tsallake wannan mummunan yanayi na cigaban al’umma,” in ji shi.

Da yake yaba wa shugaban kan kokarin da yake yi na magance matsalar rashin tsaro, Jonathan ya roki ‘yan Najeriya da su hada karfi da karfe wajen samar da kasar nan lafiya ga kowa.
Jonathan ya yi watsi da jita-jitar da ake ta yadawa cewa yana sha’awar zaben shugaban kasa na 2023, yana mai cewa hasashe ne kawai.

Ya yi alkawarin ci gaba da bauta wa Allah, bil’adama, Afirka da duniya baki daya gwargwadon ikonsa kuma da dukkan himma da sahihanci.

Ya yaba wa Gwamna Okowa saboda “gagarumar ci gaban da ya samu” ta fuskar rayuwar dan Adam da kuma samar da ababen more rayuwa.

Tsohon Shugaban ya jajantawa gwamnan kan rasuwar mahaifinsa, kuma ya bukace shi da ‘yan uwansa da su ci gaba da inganta abubuwan da mahaifinsu ke so a matsayin wata hanya ta rashin shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *