Har yanzu Buhari bai maye gurbin ministocin da suka yi murabus ba – duk da alkawarin da ya yi na gaggauta maye gurbinsu.

A yayin wani zama da aka gudanar a ranar 13 ga Mayu ga ministoci masu barin gado masu neman mukamai, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa zai maye gurbinsu cikin gaggawa.

Kwanaki kadan gabanin zaman, Buhari ya bukaci dukkan mambobin majalisarsa da ke neman mukamai da su sauka daga mukamansu.

Umurnin shugaban ya zo ne biyo bayan kiraye-kirayen da aka yi na yin murabus daga mukaman siyasa ga masu muradin 2023.

Bukatar murabus din nasu wani bangare ya kara ruruwa saboda damuwa game da iya tafiyar da ma’aikatunsu yadda ya kamata yayin yakin neman zabe.

Wani dalili da ya jawo cece-kuce na janyewarsu daga ofis shine tanadin sashe na 84(12) na dokar zabe ta 2022.

Sashe na 84 (12) na dokar ya ce: “Babu wani ɗan siyasa a kowane mataki da zai zama wakili mai jefa ƙuri’a ko a zaɓe shi a babban taro ko taron jam’iyyar siyasa don gabatar da ‘yan takara a kowane zaɓe.” Kotun daukaka kara ta ayyana sashe a matsayin wanda ya saba wa kundin tsarin mulki amma an tura karar zuwa kotun koli don yanke hukunci na karshe.

A lokacin zaman majalisar ministocin da abin ya shafa sun hada da Abubakar Malami, babban lauyan gwamnatin tarayya; Rotimi Amaechi, ministan sufuri; Godswill Akpabio, ministan harkokin Neja Delta, Timipre Sylva, karamar ministar man fetur, Pauline Tallen, ministar harkokin mata da cigaban jama’a.

Sauran sun hada da Chris Ngige, ministan kwadago; Uche Ogah, ministan ma’adinai da karafa; Ogbonnaya Onu, ministan kimiyya da fasaha; Chukwuemeka Nwajiuba, karamin ministan ilimi, da Tayo Alasoadura, karamin minista mai kula da harkokin Neja Delta.

Bayan haka, wasu daga cikin ministocin sun yi kaurin suna wajen yin watsi da burinsu na siyasa na ci gaba da rike mukamansu na minista.

Ministocin da ke cikin wannan rukuni su ne Malami, Pauline, Ngige, da Sylva – amma irin su Akpabio, Amaechi, Ogah, Nwajiuba, Alasoadura da Onu sun cimma burinsu.

A yayin da Akpabio, Onu, Nwajiuba, da Amaechi suka yi murabus don neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Ogah ya fafata a zaben fidda gwani na gwamnan jihar Abia, Alasoadura kuma ya tsaya takarar sanatan APC a Ondo ta tsakiya.

Ameachi, Onu, da Nwajiuba sun sha kaye a zaben fidda gwani na takarar shugaban kasa a hannun Bola Tinubu yayin da Alasoadura ya sha kaye a zaben fidda gwani na sanata na APC sannan Ogar ya lashe zaben fidda gwani na gwamnan jihar Abia na APC.

Duk da tabbacin da Buhari ya bayar na cewa zai maye gurbin ministoci masu barin gado “ba tare da bata lokaci ba, bayan wata daya, ma’aikatu shida ba su da ministoci, kuma jam’iyyun siyasa sun kammala zaben fidda gwani.

Mukamai shida da ba kowa ba, sun hada da karamin ministan ilimi, ministan sufuri, ministan harkokin Neja Delta, karamin ministan harkokin Niger Delta, da ministan ma’adinai da karafa, da kimiyya da fasaha.

One thought on “Har yanzu Buhari bai maye gurbin ministocin da suka yi murabus ba – duk da alkawarin da ya yi na gaggauta maye gurbinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *