Harin da ‘yan ta’adda Suka Kai a cocin Haske Dake karamar Chikun ya Matukar girgiza ni ~Sanata Uba sani.

A sakonsa na ta’aziya game da Harin ta’addanci da Wasu ‘yan ta’adda Suka Kai a coci Dake karamar hukumar Chikun a jihar kaduna sanatan
Ya nuna alhini tare da tausayawa Al’ummar Garin inda Sanatan yake Cewa Ina mai tausaya wa dangin wadanda suka rasa rayukansu a mummunan harin da aka kai a Cocin Haske Baptist da ke Kauyen Manini Tasha, Unguwar Kuriga, karamar Hukumar Chikun ta Jiharmu ta Kaduna.

Ina rokon Allah ya jikan Wannan bawan da maharan suka kashe kuma ya dawo da wadanda aka sace lafiya. Dole ne mu dauki matakin yaki ga wadannan masu kisan kai tare da maido da zaman lafiya da tsaro ga al’ummominmu. Inji Sanatan..

Mai martaba Sanata Mal Uba Sani

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *