Haryanzu ni dan Jam’iyar PDP ne ban koma APC ba ~Feni-Femi Kayode.

Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode ya musanta shiga jam’iyyar All Progressive Congress, APC.

Ku tuna cewa Gwamna Yahaya Bello na Kogi ya bayyana cewa tsohon Ministan Jirgin Sama ya fice daga PDP, bayan ganawarsa da Gwamna Mai Mala-Buni, abin da ya haifar da rade-radin cewa ya sauya sheka zuwa jam’iyya mai mulki.
A cikin hanzarin amsawa, Fani-Kayode ya yarda cewa lallai yana tattaunawa a duk sassan jam’iyyar.

Amma, ya bayyana karara cewa bai bar PDP ba.

“Duk da cewa mun yi taro a sassan jam’iyyun kuma muna cikin lokacin tattaunawa na siyasa, ban bar PDP ba,” ya rubuta a shafinsa na Twitter da ya tabbatar a ranar Laraba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *