Hukumar EFCC Reshen Jihar Kano Ta Kama Kudinmu Har Sama da Naira Miliyan 250 A Filin Jirgi Na Kano, Koken ‘Yan Kasuwa Ga Salami Akan EFCC Da Magu.

`Yan Kasuwan Kano Sun Kai Kokensu gaban Kwamitin Ayo Salami, Kan EFCC.

`Yan Kasuwar Chanji na Kamfanin AL-AMANA CHANGE, Dake Kano Sun kai kokensu gaban Kwamimitin Sauraron Korafe Korafe Kan Hukumar EFCC da korarren Shugabanta Ibramim Magu, wanda Mai Shara’a Ayo Salami yake Jagoranta.

Masu Chanjin sun Gabatar da kokensu, Inda Sukace Hukumar EFCC Reshen Jihar Kano ta kama Kudinsu Har Sama da Naira Miliyan 250, a Filin Sauka da tashin jiragen Sama a Kano, lamarin ya faru ne tun a shekarar 2016.

“Sunce Sunzo da kudin daga saudiya zuwa Kano domin Su Chanza Sai suka Taras Dala ta tashi Sai suka yanke Shawarar koma da kudin Saudiya, Bayan Sun Sanar da mahukuntan Saudiya zasu dawo da kudi an amince, Sai suka je Filin Jirgi na Kano Kafin Su karasa Ofishin Da zasu Sanar zasu fita da kudi Kwatsam Sai Ma’aikatan EFCC suka Kama Kudin da Mai Kudin Suka kai Ofishinsu.

Wanda yazo da kudin Ya tabbatar musu kudinsu na kasuwanci ne bana Gwamnati ba Amma Basu saurare shi ba, Suka Tsareshi Sati guda kana Suka bada Belinsa.

Shugaban Kamfanin Chanjin Alhaji Nasuru, Ya je Abuja wajen Ibrahim Magu, ya sanar dashi Halinda suke ciki da Hukumarsa ta Kano, Hakan ya sanya Mugu ya Kira Shugaban EFCC ta Kano ta wancan lokacin Cewa, masu kamfanin Chanjin Kudin nan Sunzo wajena domin haka Kuyi musu abinda ya dace.

Sai sukace zasu Gurfanar da Masu kudin a gaban kuliya, Suka gurfanar dasu kotu tace Masu kudin su Biya tarar kudi Naira dubu dari ko zaman kaso na shekaru biyu, Suka biya Tarar, Sannan EFCC ta tilastasu Sai Sun bada Rabin kudin da Suka Kama, Suka Amince Aka basu Rabi, Kotu ta Umarci EFCC da su Sanya Kudin Sama da Miliyan Dari da Hamsin a asusun bai daya Na Kwamnatin Tarayya cikin Makonni 2 bayan Amsar kudin daga Hannun masu chanjin.

Hukumar bata Sanya kudin ba Sama da Shekaru 4 sai yanzu da aka sauke, Magu Shugaba Buhari ya Kafa kwamiti da zasu Binciki Irin Ta’asar da Ake zargin Ibrahim Magu da Hukumar Tayi.

Kwamitin ya bada dama duk wanda yake da Korafi mai Hujja kan Magu ko EFCC ya Gabatar da Korafi kofa bude take Inji Shugaban Kwamitin Mai Shara’a Ayo Salami.

Hakan ya sanya Kamfanin Masu Chanjin Suka kai Kokensu Gaban Gwamitin domin adawo musu da kudinsu tunda ba na Sata bane, Sana’ar Chanji Suke sama da Shekaru 29 Sana’ar su kenan.

Hakan ya sanya Yanzu Kuma EFCC ta Kano ta nemi kotu ta bata dama ta sanya wannan kudin a asusun bai daya na Gwamnatin Tarayya, Sai dai Kotu taki basu damar sanya Kudin Tunda Basu sanya kudin ba lokacinda Aka umarcesu sai yanzu da Sukaga Bincike zaibi ta kansu.

Ya Zuwa yanzu dai Kwamitin ya Gano Ibrahim Magu ya Lakume Kudi sama da Naira Biliyan 30 da Gidaje na Alfarma Har guda 321.

Kuma Har yanzu ba’a kammala Binciken ba.

Zamu ci gaba da Kawo muku abinda Kwamitin ya bankado….

Ahmed T. Adam Bagas

Leave a Reply

Your email address will not be published.