Labarai

Hukumar EFCC ta kwato tallafin mai Naira Biliyan 13 da aka biya ba bisa ka’ida ba

Spread the love

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta kwato kusan N13bn daga kudaden da aka biya ba bisa ka’ida ba a karkashin tsarin tallafin mai tsakanin 2017 da 2021.

Rahoton hakan na cikin wata takarda da aka samu kwanan nan daga sashin kula da harkokin kudi na Najeriya, NFIU a yanar gizo kan kididdigar kasadar hadarin da ke tattare da halasta kudaden haramun a bangaren fitar da kudaden Najeriya.

“Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, hukumar da ke da alhakin gudanar da bincike da kuma gurfanar da masu hannu kan badakalar cin hanci da rashawa a harkar mai da iskar gas a Najeriya, ta kwato N12,998,963,178.29 a matsayin kudaden da aka biya ba bisa ka’ida ba a cikin tsarin tallafin tsakanin 2017 da 2021,” takardar ta bayyana. .

Almundahanar tallafin man fetur ya kasance abin damuwa a Najeriya. Misali, Bankin Duniya ya ce karin tallafin man fetur ya jefa tattalin arzikin Najeriya cikin hadari domin biyan tallafin na iya yin tasiri sosai ga kudaden gwamnati da kuma haifar da matsalolin dorewar bashi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button