Labarai

Hukumar EFCC Tayi Awon Gaba da Murtala Sule Garo.

Spread the love

Hukumar Yaki da yiwa tattalin arzikin ta’annati da zagon Kasa ta EFCC ta damke kwamishanan kananan Hukumomi ta Jihar Kano, Hon. Murtala Garo, bisa mallakan wasu dukiyoyi masu tarin Yawa Ba bisa ka’ida Ba.

Garo, na amsa tambayoyi hannun jami’an EFCC – An bayyana cewa kwamishanan na amsa tambayoyi ne bisa mallakan wasu manyan dukiyoyi a Kano da Abuja Kakakin hukumar EFCC, Dele Oyewale, ya tabbatar da labarin cewa lallai an gayyaceshi Wani rahoton Daily Nigerian ya nuna cewa kwamishanan kananan hukumomi na jihar Kano, Hon. Garo, na amsa tambayoyi hannun jami’an hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC.

Majiya ta bayyana cewa hukumar yaki da rashawan jihar Kano ta gayyaci kwamishanan yayi bayani kan dukiyokokin da ya mallaka na gidaje, motoci, gidajen mai, da sauransu. Wannan ya biyo bayan yabawan da wata kungiya mai zaman kanta, Centre for Public Trust (CPT), ta yiwa gwamna Abdullahi Ganduje, bisa kafa kwalejin yaki da rashawa a jihar.

A wasikar ta (CPT) da ta aike masa, kungiyar ya taya gwamnan murna bisa abinda suka siffanta matsayin matakin da ya dace wajen sauya tsarin mulki a jihar.

Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button