Hukumar SSS sun saki Dakta Usman Bugaje

Hukumar SSS sun saki Usman Bugaje Bakatsinen da su ka tsare saboda zazzafar caccakar Buhari

Jami’an SSS sun shafe sa’o’i takwas tsare da fitaccen ɗan siyasa Usman Bugaje, wanda su ka tsare saboda wata tattaunawa da aka yi da shi a gidan talbijin na AIT.

Majiyar kusa da Bugaje ta sanar cewa ya kai kan sa ofishin SSS na hedikwatar su da ke Abuja, ranar Laraba wajen karfe 10 na safe.

Bugaje dai Bakatsine ne da ya ki karɓar tayin muƙamin jakadan Najeriya, wanda Shugaba Muhammadu Buhari yayi masa cikin shekaran 2016.

An tsare shi ana yi masa tambayoyi tsawon sa’o’i takwas a ofishin SSS, Hedikwatar Abuja.

Rahotanni sun nuna cewa an saki Bugaje ya tafi gida wajen karfe 7 na yamma bayan an bayar da belin sa a ranar Laraba.

Wani makusanci Bugaje ya ce an gayyace shi ofishin SSS din tun makonni biyu da su ka gabata, bayan an yi wata tattaunawa da shi a gidan talbijin na AIT, a Abuja.

“An yi hira da Bugaje a wani shiri inda ya fito har sau biyu cikin makonni biyu da su ka gabata a Gidan Talbijin na AIT.

“Bayan fitowar biyu da ya yi ne sai SSS su ka gayyace shi, domin wai ya bayar da karin haske a kan wasu kalamai da ya yi a cikin tattaunawar da aka yi da shi a AIT.”

Bugaje ƙusa ne daga cikin dattawan Arewa ƴan boko kuma ƴan siyasa.

Ya yi aiki tare da gwamnatin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.

Cikin 2016 Buhari ya naɗa shi jakadan Najeriya, amma ya watsar ya ce ba ya so, tun kafin a rasa masa sunan kasar da za a tura shi.

Ya ce ya watsar da tayin ne domin ya na da wani shiri na kafa wata tafiya domin ceto Arewacin Najeriya, tafiyar da ya kira “Arewa Research and Development Project (ARDP).”

Kokarin jin ta bakin Kakakin Yada Labarai na SSS, Peter Afunanya, ya ci tura, saboda bai dauki waya ko amsa sakon ‘text’ ba.

Daga Mutawakkil Gambo Doko

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *