Labarai

Hukumar ‘yan Sandan PSC tayi Watsi da Binciken Kwamitin Bincike kan DCP Abba kyari.

Spread the love

A ranar Larabar da ta gabata ne dai hukumar ‘yan sandan ta gano wasu kura-kurai a cikin rahoton binciken da DIG Joseph Egbunike ya jagoranci kwamitin binciken da ya gabatar kan zargin da ake yi na kwamandan IRT, DCP Abba Kyari kan badakalar dala miliyan $1.1 na damfarar yanar gizo kan badakalar Mista Ramon Abbass wanda aka Fi sani da Hushpuppi.

Sakamakon haka, Hukumar ta mayar da rahoton binciken zuwa ga IGP Usman Alkali Baba domin ci gaba da bincike da kuma fayyace dangane da takamaiman tuhumar da hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka ta keyi kan batun.

A wani taron manema labarai a ranar 21 ga Disamba, 2021, kwamishinan yada labarai da wayar da kan jama’a na PSC, Mista Austin Braimoh, lokacin da yake magana kan batutuwan da suka shafi ladabtarwa da kuma lokacin da aka gurfanar da jami’an ‘yan sanda ciki har da Abba Kyari, Yace za a sake duba lamarin tare da sanya takunkumi, ya bayyana. cewa shari’ar ladabtarwa da kuma makomar DCP Abba Kyari wanda aka mika rahoton bincikensa ga hukumar za a gama shi a watan Janairu zuwa Fabrairu 2022 daga hukumar kuma za a yanke hukunci na karshe.

Braimoh ya ce, “Akwai shari’o’in ladabtarwa dake kasa da dama da suka shafi jami’ai kuma hukumar ‘yan sanda za ta bincike su don haka Hukumar PSC ba za ta kafa wani kwamitin na daban da zai yi shari’a ko Binciken DCP Abba Kyari ba

Majalisar Kwamitin hukumarmu ba zai tattauna batun da’ar jami’ai ga wani officer mutun daya ba a a. Za ayi bincike tare da sauran shari’o’in ladabtarwa na wasu jami’an da ke da matsala. Za a yanke shari’ar Kyari tare da sauran su bayan an yi la’akari da komai kan batun daya shafe su Ba ma daukar banbanta matakin ladabtarwa kan ko wanne Jami namu.

Ya ce, “An dage zaman na sashin ladabtarwa har zuwa watan Fabrairun 2022. Yau Abin da muka tattauna shi ne batun karin girma da daukaka kara.

Dangane da Abba Kyari, wata majiya a hukumar ta shaida wa Vanguard cewa hukumar PSC ta mayar da rahoton kwamitin binciken daya samu goyon bayan shawarar ofishin ministan shari’a Abubakar Malami wanda ofishin hukumar ta mayar da rahoton kwamitin bayan karbar rahoton. daga IGP Usman Alkali.

Domin cim ma zaman taron da aka shirya gudanarwa inda za a tattauna batutuwan da suka shafi ladabtarwa da kuma wasu laifukan da suka shafi jami’an ‘yan sanda da kuma yanke hukunci, an ce hukumar ta PSC ta baiwa hedikwatar rundunar wa’adin kwanaki 14 da ta kammala wannan sabon bita domin kawo karshen lamarin.

Kuna Iya tunawa cewa an dakatar da DCP Abba Kyari ne a watan Yulin 2021 kan zargin damfarar Hushpuppi bayan an tambaye shi, don ba da damar gudanar da bincike ba tare da tsangwama ba sannan aka maye gurbinsa da DCP Tunji Disu a matsayin Kwamandan IRT.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button