Hukumomin Najeriya sun haramta sallar idi a wasu masallatai

Covid-19 ta tilasta Najeriya haramta sallar Idi a wasu masallatai

Sakamakon barazanar dawowar cutar covid-19 a Najeriya, ministan babban birnin kasar Muhammad Bello ya haramta Sallar Idi a Masallachin Idin da ke kan hanyar Umaru Musa Yar’Adua.

Sanarwar da Sakataren yada labaran sa Anthony Ogunleye ya rabawa manema labarai ta ce an dauki matsayin ne bayan ganawar da aka yi tsakanin tawagar limaman Abuja da kuma hukumomin birnin.

Sanarwar ta ce an bukaci Masallata da su gudanar da Sallar Idi a wajen Masallatan Juma’ar su, kuma kar su wuce kashi 50 na mutanen da suka saba zuwa Masallachin.

An kuma bukaci shugabannin addinin da su tsara yadda jama’ar za su gudanar da ibadar ba tare da samun cunkoson da zai haifar da matsala ba.

Hukumomin sun kuma haramta ziyarar wuraren shakatawa domin dakile yaduwar cutar.

Daga Mutawakkil Gambo Doko

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *