Labarai

IBB ya tsallake zuwa Kasar Jamus Kuma ba zai dawo ba sai Shugaba Buhari ya sauka a mulkin Nageriya.

Spread the love

Tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) ya fita kasar waje domin duba lafiyarsa na yau da kullum, kuma ana sa ran zai dawo kasar bayan kammala babban zabe.

An ce ya tashi daga kasar ranar Asabar zuwa Jamus domin duba lafiyarsa na yau da kullum.

Wakilinmu ya tattaro mana cewa ya tashi daga filin jirgin sama na Minna zuwa filin jirgin Nnamdi Azikwe, Abuja inda aka dauke shi a cikin wani jirgin sama mai zaman kansa zuwa kasar.

An ce ya samu rakiyar dansa na biyu, Aminu da wani jami’in tsaro. Wata majiya mai tushe ta shaida wa Wakilinmu cewa a halin yanzu tsohon Shugaban Sojan na kasar Switzerland.

Sai dai ba a sani ba ko ‘yan uwansa na kusa za su bi shi zuwa Jamus daga baya.

Daya daga cikin masu magana da yawun Janar,  Alhaji Mahmud Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya kara da cewa anyi tafiyar ne kawai domin duba lafiyar sa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button