Labarai

Idan na Zama Gwamna zan gudanar da Gwamnati dunkulalliya amatsayin al’umma daya a jihar Kaduna ~Cewar Sanata Uba sani.

Spread the love

Sanata Uba sani ya bayyana hakan ne a Lokacin wani taro na masu ruwa da tsaki na jam’iyar APC Wanda Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru EL’rufa’i ya Sami halarta Sanatan ya dage da cewa Shirin mu tashi zuwa shiyyar Sanatan Kaduna ta tsakiya a yayin da na kasance tare da Gwamna Nasir El-Rufai da abokiyar takarara ta kuma mataimakiyar gwamna, Dakta Hadiza Balarabe a wajen taron jam’iyyar APC na shiyyar 2.

Taron wanda ya dauki hankulan mutane sosai, ya karbi bakuncin shugabannin siyasa da na gargajiya da na addini, ’yan kasuwa, kungiyoyin farar hula, kungiyoyin matasa da mata, nakasassu (PWDs) da sauran kungiyoyin da suka shafi al’ummarmu.

Taron ya kasance mai fa’ida, gaskiya da haɓakawa kwarai kuma tabbas zai Yi jagoranci zuwa ga Kudrin manufofin mu.

A yayin da muke ci gaba da yakin neman zaben da ya shafi batutuwan al’umma ina amfani da wannan damar wajen sake tabbatar wa al’ummar Jihar Kaduna nagari cewa za mu gudanar da gwamnati mai Ha’din Kai amatsayin dunkulalliyar al’umma Daya.

Masana da dama suna hasashen cewa Sanata Uba sani shine zai Zama Gwamnan jihar Kaduna a zaben 2023 Mai zuwa duba da yanayin karbuwarsa ga al’umma.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button