Labarai

Ina fatan dawowa Daura nan da wata 5 – Buhari

Spread the love

Shugaban kasa Muhamamdu Buhari a ranar Talata a Abuja ya karbi bakuncin ‘yan kungiyar Jam’iyyatu Ansaridden (Attijaniyya), inda ya yabawa kungiyar Musulunci kan yadda ake ci gaba da yin hakuri da addini a kasar.

Shugaban ya shaida wa kungiyar karkashin jagorancin Sheikh Muhammad Khalifa Niass, Khalifan Jam’iyyatu Ansaridden (Attijaniyya) cewa ya yaba da irin rawar da suke takawa wajen samar da zaman lafiya a kasashen Afirka da dama.

Shugaba Buhari wanda ya mika godiyarsa ga ‘ya’yan kungiyar bisa addu’o’in da suke yi wa gwamnatinsa da kuma kasa, a wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban, Garba Shehu ya fitar, ya ce yana fatan komawa garin Daura nan da watanni biyar masu zuwa karshen wa’adinsa a ofis.

A yayin ziyarar ban girma da kungiyar ta kai Sheikh Tijjani Shehul Hadi Almauritany ya gabatar da addu’o’i ga shugaban kasa da kasa da kuma ‘yan Najeriya yayin da Sheikh Abdullahi Lamine ya gudanar da karatun kur’ani mai tsarki.

A nasa jawabin, Khalifan kungiyar, Sheikh Niass, ya ja hankali kan tarihin Manzon Allah SAW, da irin darussan da musulmi za su iya yi daga tsarin rayuwarsa.

Da yake jaddada wajibcin tuba na gaske, kamar yadda koyarwar kur’ani mai tsarki ta bayyana, Sheikh Niass ya yi alkawarin cewa kungiyar Attijaniyya za ta ci gaba da tabbatar da zaman lafiya da hadin kai, kamar yadda koyarwar Littafi Mai Tsarki da Musulunci suka tanada.

Khalifah Niass ya kuma ba da labarin irin kusancin da mahaifinsa, Sheikh Ibrahim Niass ya yi da Nijeriya da al’ummarta, wanda ya kai shekaru saba’in, inda ya ce iyalan sun kuduri aniyar ci gaba da kulla alaka.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button