Inajin Daɗin Yadda Kiristoci da Musulmi Ke Taya Junansu Murna, ~ Inji Buhari

Shugaban Ƙasa Buhari ya bayyana jin daɗinsa ganin yadda kiristoci ke bada kyauta tare da shan ruwa tare da yan uwansu musulmai a lokacin azumin watan Ramadan.

Buhari yace hakan na nuni da yadda mabiya addinan biyu ke son junansu, da kuma yan uwantakar dake tsakaninsu, kuma hakan na sa shugaban farin ciki Matuƙa.

Daga Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *