
Bayan kwashe kwanaki ba tare da jin duriyarta a shafin sada zumintar zamani na Instagram daga karshe dai jaruma Aisha Aliyu Tsamiya ta bayyana da wani Sabon account inda jarumar ta tabbatar da cewa Kwamfanin Instagram ne suka kulle account din nata amma bata bayyana dalilin faruwar hakan ba, Jaruma Tsamiya tayi asarar shafin nata bayan ta Shahara ta hanyarsa, shafin nata wanda aka kulle Mai suna RealAishaAliyu Yana dauke da jama’a sama da mutun milyan biyu 2m. amma Kwamfanin Instagram sun kulle shi
Jarumar ta bude Sabon shafi Kuma Jama’arta masoya sun fara bibiyar ta Kawo yanzu dai ta samu mabiya sama da dubu dari biyar 500k Tsamiya ta wallafa sabbin bidiyo da hotuna domin tallata Sabon shafin nata Mai suna Realaeeshatsamiya_Backup ga masoyan ta inda take rubutawa masoyan na ta a harshen turanci da cewa please Follow my new account, ma’ana ku biyo ni ta hanyar Sabon account Dina.
Jaruma Aisha Aliyu Tsamiya tana daga cikin jerin fitattun jarumai da ake gani da mutunci a masana’antar ta kanywood.