Labarai

Irin Tarihin mu daya da Gawuna ~Cewar Ganduje.

Spread the love

Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana hakan a wajen yakin neman zaben jam’iyar APC a karamar hukumar Gaya a wani gajeran Bidiyo an hango Gwamnan Yana yabon Dan takarar Gwamnan jihar Kano a karkashin jam’iyar ta APC Dr Nasiru Yusuf Gawuna cewa wannan Mai saje, sajen Alkhairi ne ku saurara kuji Tarihin sa tarihin sa irin nawa tarihin ne gogewarsa irin tawa ce martabarsa Irin tawa ce mutunci sa irin nawa ne.

Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje shine Wanda faifain bidiyon sa ya bayyana a idon duniya a Lokacin da yake saka dalolin Amurka a babbar Riga Jaridar Daily Nigerian ce ta Fitar da Bidiyon a shekara ta 2023.

Dr Nasiru Yusuf Gawuna shine Dan takarar Gwamnan jihar Kano Wanda Ganduje ya tsayar amatsayin Wanda zai gajeshi bayan zaben 2023.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button