Jami’an tsaro sun ku6utar da Aisha wacce iyayenta suka kulle tsawon shekaru 10

Jami’an tsaro a birnin Kano sun ku6utar da wata matashiya Aisha Jibrin mai shekaru 15 da iyayenta su ka daure ta a wani daki na tsawon shekaru 10.

Kakakin Rundunar ‘yan sandan jihar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce wasu ne suka taimaka masu da bayanan abin da ke faruwa kuma nan ta ke su ka yi dirar mikiya a unguwar Darerawa Quarters da ke Fagge inda suka ku6uto da matashiyar kuma su ka kai ta asibiti.

DSP Kiyawa ya ce tuni ‘yan sanda su ka carke mahaifiyar matashiyar a yayin da su ke ci gaba da neman mahaifin yarinyar wanda ya gudu don tsoron haduwa da hukuma.”

Ahmad Aminu Kado..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *