Jami’ar Amurka East Corolina Ta nemi Afuwar Ganduje Kan bashi Farfesan Bogi

Jami’ar East Carolina ta nuna nadama kan duk wani abin kunyar da ka iya faruwa sakamakon cece-kucen kwana nan game da nadin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano a matsayin Farfesa kuma Babban Malami A bangaren koyar da Dabarun jagoranci A 30 ga nuwamba, 2020 .

A cikin amsar wasiƙar da gwamnatin jihar Kano ta aika kan batun kuma aka aika wa gwamnan, jami’ar ta kuma amince da nasarorin da gwamnan ya samu a fannin ilimi, tana mai cewa “Ya chanchanta Yazama malami.

Wasikar wacce sa hannun shugaban rikon kwarya kuma babban mataimakin shugaban jami’ar kan harkokin ilimi, Dakta B. Grant Hayes, ta ce abin da wasikar ta rubuta tun farko da aka aike wa gwamnan ba nufin jami’ar ba ce ta haifar da wani abin kunya.

“Munyi nadamar cewa wannan yanayin ya haifar da wani abin kunya, kasancewar hakan ba niyyar Jami’ar Carolina ba ce, kuma ba shi ne dalilin wasikata ba,” in ji ta.

DAGA Abdulrashid Abdullahi,Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published.