Jerry Gana Ya Yi Barazanar Maka Majalisar Ƙolin Musuluncin Nigeria a Kotu

Tsohon ministan sadarwa Jerry Gana na ya bukaci majalisar kolin addinin musulunci da ta janye kalamanta a kansa.

Gana ta bakin lauyansa ya ce ba shi da alaka ta kusa ko nesa da Muhammad Yusuf wanda wanda ya kafa Boko Haram.

Tsohon ministan ya ce muddin majalisar kolin musuluncin bata janye maganar ba zai maka ta a gaban kuliya Jerry Gana, tsohon ministan sadarwar, ya bukaci majalisar kolin harkokin addinin musulunci (NSCIA) da ta janye kalamanta da suka alakanta shi da Mohammed Yusuf, wanda ya fara kafa Boko Haram.

NSCIA, yayin da take kare Isa Pantami, ministan sadarwa, wanda ke fuskantar matsin lamba saboda ya taba goyon bayan wasu kungoyoyin ta’addanci, sun yu ikirarin cewa akwai wani kirista wanda yake minista ne a lokacin, ya yi belin Muhammad Yusuf har sau uku a 2008.

Duk da NSCIA bata ambaci sunan ministan ba, Jeo-Kyari Gadzama mai lambar (SAN) kuma lauyan gana, a wata takarda da ya aike wa NSCIA mai kwanan watan 29 ga april, 2021, yace mutane sun san da wanda yake karewa ake.

Ya tabbatar da cewa Gana bashi da alaka da wanda ya kafa Boko Haram din. “Muna sanarwa, a madadin wanda muke wakilta, sabanin rahoton karya da aka yada, wanda muke karewa bai taba, ta kowacce irin fuska yin belin Malam Muhamad Yusuf ba” kamar yadda sanarwar ta ce.

“Wanda muke karewa bashi da alaka, ta kusa ko ta nesa da Yusuf, kuma basu taba zama tare ba, ba abokai bane, kuma baya goyon bayan Boko Haram kamar yadda NSCIA tayi zargi.”

Lauyan ya kara da cewa kamar yadda kuka sani lamarin ya yi nisa a kafafen sadarwa na zamani har ma ya zama abun tattaunawa tsakanin mutane, yasa akwai bukatar sanar da mutane Gana ba dan Ta’adda bane.

Ya kuma bukaci da NSCIA da ta janye kalamanta ko kuma su dauki matakin Shariah

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *