Jirgin Kasa Da Ya Taso Daga Legas Zuwa Zariya Ya Yi Hatsari a Jihar Kaduna

Wani Jirgin kasa da ya taso daga Legas ya kauce daga kan hanyarsa a wani yankin jihar Kaduna.

An ruwaito cewa, babu asarar rai, kuma tuni hukumar kula da jiragen kasa ta fara aikin gyara.

Rahoton ya bayyana cewa, wasu bata-gari ne a suka lalata hanyar jirgin wanda ya jawo hatsarin Wani jirgin kasa mai dauke da bututun ruwa daga jihar Legas zuwa Zariya a jihar Kaduna ya yi hatsari a wani yankin jihar ta Kaduna.

Hatsarin wanda ya afku a yankin Unguwar Kanawa da ke Kaduna ya tilasta wa jirgin tashi daga layin dogo, wanda hakan ya sa biyar daga cikin taragon jirgin kaucewa daga kan hanyar

Duk da cewa ba a samu asarar rayuka ba a lamarin, injiniyan da ke kula da ayyukan Arewa na kamfanin jirgin kasa na Najeriya, Haruna Ahmed ya shaida wa gidan talabijin na Channels cewa hatsarin jirgin ya faru ne sakamakon lalata hanyoyin jirgin da wasu bata-gari suka yi.

Ya yi bayanin cewa, tuni Kamfanin Kula da Jiragen Kasa ya fara aikin kwashe sauran taragon da ba su fado daga kan hanya ba, yayin da ayyukan gyaran hanyoyin za su biyo baya nan gaba.

Daga Ahmad Aminu Kado

One thought on “Jirgin Kasa Da Ya Taso Daga Legas Zuwa Zariya Ya Yi Hatsari a Jihar Kaduna

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *