Jita-Jitan Hare-Haren Yan Bindiga Ya Kawo Hargitsi a Abuja Yayin da Iyaye Ke Janye Yara Daga Makarantu

Wani rahoto na jaridar The Guardian ya nuna cewa akwai fargaba a Abuja kan jita-jitar ‘yan fashi da ke tarewa a wajen babban birnin Najeriyar.

Babban birnin tarayya, FCT na kewaye da jihohi wadanda suka fuskanci hare-hare daga yan fashi da yan ta’adda a yankin su.

A cikin jihar Neja da ke kusa, an yi garkuwa da mutane da dama kwanakin da suka gabata daga garin Shadadi da ke karamar hukumar Mariga kusa da babban birnin Najeriya.

A cewar wani mazaunin yankin, sama da ‘yan bindiga 1,000 ne suka kai hari yankin, inda suka kashe mutane takwas tare da raunata hudu, yayin da duk wadanda suka tsira suka tsere.

Kwamishinan yada labarai na jihar Neja, Sani Idris, ya tabbatar da afkuwar harin sannan ya ce a yanzu haka suna kan tattara alkaluman mutanen da harin ya shafa.

Tuni, iyaye a Abuja, musamman a Karamar Hukumar Bwari, suka fara janye yaransu gaba daya daga makarantu kan wasu daruruwan mutane da ake zargin mayakan Fulani ne a Sabon-Wuse, wani garin kan iyaka da jihar Neja.

A cewar rahotanni, wadanda ake zargin mayakan Fulani ne da suka badda kamanni a matsayin makiyaya sun tsallaka babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna kusa da garin Sabon-Wuse a Neja a ranar Laraba, 5 ga watan Mayu lamarin da ya haifar da tashin hankali yayin da mazauna yankin suka firgita suna zaton hari ne.

Da yake martani a kan ci gaban, Ministan Babban Birnin Tarayya, Malam Muhammad Bello, ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da yin aiki tare da Sojojin Najeriya da duk sauran hukumomin tsaro don ci gaba da kare birnin na FCT.

A cewar jaridar Leadership, Ministan ya bayar da tabbacin ne lokacin da ya karbi bakuncin wata tawaga daga Hedikwatar Tsaro da ke Abuja.

Bello ya ce Abuja ta kasance cikin kwanciyar hankali saboda dangantakar aiki da ke tsakanin shugabannin rundunonin sojoji daban-daban da sauran hukumomin tsaro a babban birnin tarayya a tsawon shekaru.

Daga Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *