“Kada ka gaza” Buhari ya ce da Inspecta General.


Bayan dawowar sa daga kasar waje inda yaje aka duba lafiyar jikin sa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jaddada wa mukaddashin inspecta general akan cewa ya tashi tsaye wurin kawo tsaro a kasar Nijeriya.

Ya jawo hankalin Babbabn Jami’in tsaro na yan sanda cewa lallai kada ya kunyatar da mutanen Nijeriya wadanda suke da yakini da shi a matsayin sa na IG.

A yayin da yan jarida suka riske shi da tambayoyi a airport din Nnamdi Azikwe, Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana abubuwan da suka cancantar da inspecta general din a matsayin mukaddashin IG, a inda ya bayyana cewar shi inspecta din yana cikin wannan tsari tun ba yanzu ba kuma yana da gogewa da ake bukata wurin samarda tsaro.

Ya fada cewa “Mun duba yanayin tsari. Akwai kwamiti wanda ya taho daga ministan jami’in yan sanda, an bani wasu sunaye kuma sunansa ne ya fito a matsayin wanda aka zaba a inda ya ce

“ya san aikin sa, ya dade a cikin wannan tsari, yana da horewar da ya kamata na aikin kuma ya goge a fannin, saboda haka muna da yakini da tsamanin sosai a kansa”

Shugaba Muhammadu Buhari ya kuma jaddada cewar har ila yau suna kai wurin kokarin kawo karshen rashin tsaro kuma suna fatan iya kokarinsu zai kawo kwanciyar hankali da daidaita kasar.
Da aka tambaye shi a kan tafiyar da yayi don samun lafiyar jikin sa ya bada amsa cewa “komai ya tafi lafiya lau” sannan ya kara da cewar da dawowar sa zaya cigaba da gudanar da ayyukan sa

Jirgin shugaban kasa ya sauka a misalin karfe hudu da minti arba’in da hudu na yamma. Wadan da suka je tarbar sa sun hada da Chief of staff Ibrahim Gambari, Ministan birnin tarayya Malam Muhammed Bello da kuma Major General Babagana Manguno da sauran su.

Maryam Gidado Aminu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *