Labarai

Kafin Rahama sadau ta shiga film munyi soyayyar Free-call cikin dare har ku’din mashin nake bata a makaranta ~Cewar matashi shu’aibu Abdullahi.

Spread the love

Wani matashi wanda Freedom Radio ta yi hira da shi ya bayyana cewa sun taba soyayya da jaruma Rahama Sadau amma a baya, shafin Mutan Kannywood na Instagram ta ruwaito.

Kamar yadda yace, lokacin makarantar sakandare su daya a shekarar 2004 kuma wurin zamansu daya. 

Ya bayyana yadda yake ba ta kudi tun a lokacin kasancewar yana tsaron wani shago kuma yana dan samun kudinsa a lokacin.

Ya ce yana bata har kudin mashin da dai sauran ‘yan kyautatawa irin na saurayi da budurwa.

A cewarsa a lokacin suna tare gidansu basu sani ba gaskiya, kuma dayake iyaye da yayyinsa suna da tacewa akanshi ya ga bai sanar da su ba lokacin da ya fara soyayya da ita ba.

Wannan dalilin ne yasa soyayyar tasu bata yi tasiri ba, kuma ya hakura da batun aurenta.

Sanannen abu ne yadda jaruma Rahama Sadau tayi fice kuma take shan caccaka a kafafen sada zumuntar zamani wanda dama ba yau aka fara ba.

Jarumar ta saba yin wallafa iri-iri wadanda ke hassala mabiyanta har su dinga zaginta su na cin zarafinta da maganganu.

Akwai wadanda kan kira ta da marar kishin addini musamman ganin yadda take cudanya da mawaka da jaruman kudu.

A wannan karon, jarumar ta yi wallafa ne tana yi wa mawaki Davido ta’aziyyar mutuwar dansa Ifeanyi, wanda ya mutu a kwamin wanka ta shafinta na Twitter.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button