• About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact
JaridarMikiya
Advertisement
  • Home
    • Home – Layout 1
    • Home – Layout 2
    • Home – Layout 3
    • Home – Layout 4
    • Home – Layout 5
    • Home – Layout 6
  • Tech

    These Are the 5 Big Tech Stories to Watch in 2017

    With 150 million daily active users, Instagram Stories is launching ads

    Trending Tags

    • Nintendo Switch
    • CES 2017
    • Playstation 4 Pro
    • Mark Zuckerberg
No Result
View All Result

Home Labarai

Kalaman Batanci Ga Sanata Uba Sani APC ta Buƙaci a hukunta Kakakin dokokin Majalisar jihar kaduna ~wato Hon Zailani Yusuf.

Sabiu1 by Sabiu1
January 9, 2021
in Labarai
0
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Shugabannin jam’iyyar All Progressive Congress, (APC) na kananan hukumomi bakwai da suka hade yankin Kaduna ta Tsakiya sun yi kira da’a sanya takunkumi ga kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna, Hon. Yusuf Zailani da abokinsa, Chakis Sakamakon saba wa doka ta 21 sashin A) na kundin tsarin mulkin jam’iyyar.

Idan baku manta ba dai an kama kakakin majalisar Zailani da Chakis a cikin wani bidiyo a kwanan nan suna maganganun batanci da kalamai marasa kan gado game da Sanatan da ke wakiltar gundumar Kaduna ta Tsakiya Sanata Uba Sani, wanda shugabannin APC Suka dauka a matsayin Kalaman Batanci marasa kyau kuma illa ga jam’iyyar.

Bayan tashi daga taro a ranar Juma’a, shugabannin jam’iyyar APC na kananan hukumomi bakwai Wanda Suka hada da, Gambo Shehu Haske, Alhaji Ibrahim Musa, Engr. Magaji Bala Mataz, Alhaji. Abdulahi Jariri, Alhaji Ibrahim Yakubu Soso, Alhaji Musa Sheriff da Hon. Ishaya Shagay, sunce Shugaban Majalisar da Chakis sun tsallake layi tare da maganganun da suka jawowa jam’iyyar zama abin kunya.

A wata sanarwa mai dauke da sa hannun dukkan shugabannin APC na kananan hukumomi bakwai na Chikun, Kaduna ta Kudu, Kaduna ta Arewa, Birnin Gwari, Igabi, Giwa da Kajuru bayan taron da suka yi a Kaduna, sun yi Allah wadai da kalaman tare da yin kira da a sanya takunkumi ga Shugaban Majalisar Zailani da Chakis.

Sanarwar ta ce: “Sashi na 21 A) na Kundin Tsarin Mulki na Jam’iyyar ta APC ya bayyana laifukan su da kuma hukuncin su kuma abin da su biyun suka yi ya dace da laifukan karamin sashe na 1, 11, V da VII.

Shugabanin sun Kara da Cewa Dangane da abin da ke sama, mu shugabannin jam’iyyar APC na kananan hukumomi bakwai na Kudancin Kaduna ta Tsakiya suka ce mun cimma matsaya kan cewa ya kamata a dauki matakan ladabtarwa a kan Kalaman da Hon. Zailani Yusuf da Hon. Aliyu Haruna Chakis sukayi a dukkan matakai, ”inji su.

Shuwagabannin Jam’iyyar sun ce sabanin ikirarin da Zailani da Chakis ke yi, Sanata. Uba Sani ta hanyar ofishinsa ya ba da dama da kuma nemawa tare da ba da rance ga jama’arsa: “Sanatan ya kuma bai wa mazabarsa karfin gwiwa ta hanyar aikin gidauniyar Uba Sani, wanda matasa da yawa suke aiki a ciki kuma mata da dama suke anfana da irin abubuwan da yakeyi.

“Sanata Uba Sani ya yi rawar gani a cikin shekara daya ta hanyar daukar nauyin wasu kudirai wadanda ke da nufin inganta rayuwar wadanda suka zabe shi. Sanata Uba Sani yana Kan aikinsa na bayar da gudummawar kafa Kwalejin Ilimi ta Tarayya a karamar Hukumar Giwa, Cibiyar Kula da Lafiya ta Tarayya da ke Rigasa wacce ke karkashin karamar hukumar Shugaban Majalisar Yusuf Zailani, kudirin ya wuce karatu na uku kuma yana jiran amincewar shugaban kasa da sauran kudurin da za su kawo ci gaban da aka rasa a yankin Sanatan.

“Sanatan ya kawo ayyuka da yawa wanda Igabi ke amfana da Ginin Kwalejin a Jami’ar Jihar Kaduna Wacce za’a Gina a darajar Naira Biliyan 2.4, da kuma samar da dakunan kwanan dalibai masu karfin 110bed a Kwalejin’ Gwamnati ta ‘Yan Mata dake Giwa da ta Sakandaren Gwamnati Birning Gwari.

“Ya kuma dauki nauyin gina Cibiyar Kwarewar na’ura Mai kwakwalwa kimanin 50000 a Birnin Gwari, Giwa, Kaduna ta Kudu da Kaduna ta Arewa. Gina Cibiyar Samun Kwarewa a Karamar Hukumar Chikun da kuma Cibiyoyin Kula da Kiwon Lafiya a matakin farko a Kasuwar Magani, Kajuru. Duk a cikin shekara Daya inji ”shugabannin na APC.

Previous Post

Sama da mutane miliyan 2 ne suka rasa Mazauninsu sakamakon ta’addanci a Najeriya – FG

Next Post

Sarkin Zazzau ya daukaka darajar mukamin sarautar Munir ja’afar Yariman Zazzau Zuwa madakin Zazzau.

Sabiu1

Sabiu1

Next Post

Sarkin Zazzau ya daukaka darajar mukamin sarautar Munir ja'afar Yariman Zazzau Zuwa madakin Zazzau.

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Stay Connected test

  • 23.6k Followers
  • 99 Subscribers
  • Trending
  • Comments
  • Latest
Burin murtala garo na zama Gwamnan Kano ya ruguje, ya hau jirgi ya bi Ganduje kasar Dubai domin neman goyon bayansa kafi ya ajiye mukamin kwamishina.

Burin murtala garo na zama Gwamnan Kano ya ruguje, ya hau jirgi ya bi Ganduje kasar Dubai domin neman goyon bayansa kafi ya ajiye mukamin kwamishina.

April 2, 2022
An garzaya da Buba Marwa Asibitin kasar London kwanaki ka’dan Bayan DIG mai Binciken DCP Abba kyari ya mutu.

An garzaya da Buba Marwa Asibitin kasar London kwanaki ka’dan Bayan DIG mai Binciken DCP Abba kyari ya mutu.

March 15, 2022
TSARO: Maganar gaskiya Buhari bashi da imani bashi da tausayi, Allah ya Isa Tsakanin mu da azzalumin Shugaba ~Cewar Ali madaki.

TSARO: Maganar gaskiya Buhari bashi da imani bashi da tausayi, Allah ya Isa Tsakanin mu da azzalumin Shugaba ~Cewar Ali madaki.

March 30, 2022
DA ‘DUMI ‘DUMI: EFCC ta gano yadda Gwamna Tambuwal yayi kwana da Naira Bilyan 189.1bn zuwa ga wasu asusun ajiyar bankuna.

DA ‘DUMI ‘DUMI: EFCC ta gano yadda Gwamna Tambuwal yayi kwana da Naira Bilyan 189.1bn zuwa ga wasu asusun ajiyar bankuna.

April 2, 2022

Ina son aure yaro matashi dan shekara 25 zuwa 30~ Inji shugabar kungiyar muryar Zawarawa ta Kano

14

CBN ya rabawa Matasa mutum sama da dubu bakwai naira Biliyan biyu da digo hudu (2.04b) a karkashin tsarin NYIF.

6

Kasuwancin Cryptocurrency Haramun ne zalla ~inji Sheikh Bin Usman.

4

Duk Wanda Ya Cika Neman Bashin Ranche Karkashin Tsarin NYIF Ya Gaggauta Shiga Dashboard, Ya Sabunta Asusun Ajiyarshi Na Banki

3
Da Dumi Dumi: ‘Yan ta’adda sun harbe daya daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, in ji mai sasantawa.

Da Dumi Dumi: Kotu ta daure Sanatan Najeriya shekaru bakwai a gidan yari bisa samunsa da laifin karkatar da kudade.

July 1, 2022
Sanatocin kasar Amurka sun bukaci a saka Najeriya a cikin jerin kasashe masu take hakkin addini.

Sanatocin kasar Amurka sun bukaci a saka Najeriya a cikin jerin kasashe masu take hakkin addini.

July 1, 2022
‘Yan ta’addan Igbo IPOB sun kashe Sharif Abubakar Isah Mayolope a jihar Anambra.

‘Yan ta’addan Igbo IPOB sun kashe Sharif Abubakar Isah Mayolope a jihar Anambra.

July 1, 2022
Yakin Rasha da Ukraine: Najeriya a shirye take ta samar da iskar gas a fadin Turai – Buhari

Yakin Rasha da Ukraine: Najeriya a shirye take ta samar da iskar gas a fadin Turai – Buhari

July 1, 2022

Recent News

We bring you the best Premium WordPress Themes that perfect for news, magazine, personal blog, etc. Check our landing page for details.

Follow Us

Browse by Category

  • Addini
  • Al'adu
  • Alqur'ani Tafarkin Tsira
  • Fina finai
  • Ilimi
  • Kasashen Ketare
  • Kasuwanci
  • Kimiya Da Fasaha
  • Kungiyoyi
  • Kunne Ya Girmi Kaka
  • Labarai
  • Lafiya
  • Mata
  • Nishadi
  • Rahotanni
  • Sana'o'i
  • Sanannu
  • Siyasa
  • Sports
  • Startup
  • Tech
  • Travel
  • Tsaro
  • Tsegumi
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • World
  • Zamani
  • Zamantakewa

Recent News

Da Dumi Dumi: ‘Yan ta’adda sun harbe daya daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, in ji mai sasantawa.

Da Dumi Dumi: Kotu ta daure Sanatan Najeriya shekaru bakwai a gidan yari bisa samunsa da laifin karkatar da kudade.

July 1, 2022
Sanatocin kasar Amurka sun bukaci a saka Najeriya a cikin jerin kasashe masu take hakkin addini.

Sanatocin kasar Amurka sun bukaci a saka Najeriya a cikin jerin kasashe masu take hakkin addini.

July 1, 2022
  • About
  • Advertise
  • Privacy & Policy
  • Contact

© 2022 JaridarMikiya - Design by NGWebDev.

No Result
View All Result

© 2022 JaridarMikiya - Design by NGWebDev.