Kan Goge Maganar Buhari Lallai Zamu Hana anfani da Shafin Twitter ~Inji Lai Mohammed

Ministan yada labarai da al’adun Najeriya Alhaji Lai Mohammad ya bayyana cewa kamfanin sada zumunta na Twitter yana nuna goyon baya ga masu tayar da kayar baya a Najeriya, kuma yaci gaba da yin hakan za’a toshe shi a duk fadin kasar.

Da yaje zantawa da manema labarai, Alhaji ya nuna rashin jin dadinsa kan goge sakon da shugaban kasar Muhammadu Buhari, ya wallafa a shafinsa na Twitter in da yake jan kunnen masu tayar da kayar baya a sassan kasar, mr Lai Mohammad ya ce sun nemi jin bahasi daga kamfanin na Twitter kan goge sakon da shugaba Buhari ya wallafa a shafinsa amman kamfanin bai ba su wata gamsassar amsa ba.

Kuma suna zarginsa da nuna goyon baya ga masu kokarin kafa kasar Biafra saboda duk irin sakonnin da suke wallafawa kamfanin ba ya goge wa amma ya goge na Shugaba Buhari, saboda haka za’a dauki matakin toshi shi daga kasar, kunji fa menene ra’ayinku shin kuna goyon bayan toshe kamfanin na Twitter a Najeriya?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *