Kano katsina da jigawa sune jihohin da sukafi yawan matalauta a Nageriya.

Katsina ita ce jiha ta 3 tare da mafi yawan matalauta a Najeriya, a cikin wani binciken da Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta yi kwanan nan, Katsina Post ta samu labarin.

A cewar binciken kamar yadda wani kamfanin kididdiga mai zaman kansa, StatiSense ya wallafa a shafinsa na Twitter, jihar Katsina na da mafi yawan matalauta miliyan 4.7m.
Binciken ya kuma nuna jihohin Kano da Jigawa ne kawai da ke da 7.7m da 5.4m mafi yawan matalauta suna sama da jihar Katsina.

Yayin da jihohin Sakkwato, Bauchi, Neja, Kaduna, Zamfara, Adamawa da Taraba duk suna kasa da Katsina a cikin jerin jihohi goma da suke da mafi yawan talakawa a Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published.