Karya ake mana Bamu ce zamu bawa Atiku takara a Zaben 2023 ba ~Inji Jam’iyar PDP.

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta karyata rahotannin kafafen yada labarai kan shirin dawo da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, a matsayin wanda ke dauke da tutar takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben 2023 Mai Zuwa.

Sakataren yada labaran Jam’iyyar na kasa, Kola Ologbondiya, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da amsa kan shirin jam’iyyar na ba Atiku tikitin, a yayin tattaunawa da manema labarai a Abuja, ranar Laraba.

Kola ya ce a matsayinsu na jam’iyya, PDP a shirye take koyaushe don kare dimokiradiyya, kuma ba za ta taba goyon baya ga tsayar da dan takara ba.

“Ba mu fara sayar da fom ba, har sai lokacin, ba mu san wadanda ke neman tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar a shekarar 2023. Bugu da ƙari, ba mu fara sayar da fom ba,” in ji shi.

A wata tattaunawa ta musamman da Daily trust, wani memba na kwamitin amintattu (BoT) kuma tsohon ministan harkokin ’yan sanda, Adamu Maina Waziri, ya ce akwai fahimtar juna tsakanin jiga-jigan jam’iyyar don rike tikitin takarar shugaban kasa a Arewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *