Karya ake mun Ban sake yankar katin Shiga jam’iyyar APC ba – In ji Dr Fatima Atiku Abubakar

Dr Fatima Atiku Abubakar ta karyata wasu kafafen yada labarai da suka bada rahoton cewa ta sabunta katinta na kasancewa mamba a jam’iyyar APC.
Dr Fatima wadda diya ce ga tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Atiku Abubakar ta ce, a shekara ta 2015 ta karbi mukamin Kwamishina mai kula da kiwon lafiya, saboda haka, ya zama wajibi ta kasance mai dauke da katin jam’iyya mai mulki a wancan lokaci.
Ta ci gaba da cewa, tun lokacin da ta kammala bada gudummawarta a matsayin Kwamishina, sai ta koma gudanar da harkokin sana’arta ta gashin kanta ba tare da ta jingina da wata jam’iyya ta siyasa ba.
Dr Fatima ta ce, ta yi mamaki matuka da ta samu kagaggen labarin cewa ta sabunta rajistar zama mamba a jam’iyyar APC.
Ta jaddada cewa bata sabunta rajistar ta ba wadda ta yi amfani da ita wajen sadaukar da kai da ta yi a shekarar 2015.
Dr Fatima ta ce, “Babu shakka ina Abuja. Ban yi tafiya zuwa Jada ba kamar yadda kagaggen labarin ya zo cewa can ne na sabunta rajistar kuma ni ban cika, ko sa hannu a kowacce irin takarda ba. Takardun da ake yawo da su wai na sa hannu ban san da su ba. Na bogi ne.”
Ina fata za a dauki duk wani rahoto da yake nuna cewa na sabunta rajistar zama mamba a jam’iyyar APC a matsayin zuki-ta-malle, in ji Dr Fatima Atiku Abubakar.

Dr Fatima Atiku Abubakar
Abuja
24th February, 2021

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *