Kasar Amurka na zargin Pantami da daukar nauyin ta’addanci.

Kasar Amurka ta saka Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki, Sheikh Isa Ali Pantami cikin wanda take sakawa ido bisa sargin daukar nauyin ta’addanci.

Independent da Jaridar journalist sun ruwaito cewa, Kasar ta Amurka ta yi zargin cewa Sheikh Pantami na da alaka da Shugaban Boko Haram da aka kashe, Watau Muhamad Yusuf.

Sannan kuma yana da alaka da Abu Quatada Al Falasimi wanda babbane a kungiyar Alqaeda, an jishi yana jinjina masa. Hakanan Kasar Amurka ta zargi Shaikh Pantami da Yabon Abu Musab Al Zarqawi wanda shima daga baya ya shiga kungiyar Alqaeda a kasar Afghanistan.

0 thoughts on “Kasar Amurka na zargin Pantami da daukar nauyin ta’addanci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *