Kashe ɗan Fulani, kamar cin bashi ne, dole ka biya wata rana — El-Rufai

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya zunguro sama da kara a wajen ƴan Najeriyar Kudu akan batun da yayi na dalilin da yasa ake yawan samun tada ƙayar baya daga Fulani wanda hakan ke kaiwa ga kashe kashe na ɗaukar fansa, garkuwa da mutane da dai sauransu.


A cewar gwamnan ɗan jam’iyyar APC, ya tabbatar da cewa, idan har za’a kashe ba fullatani, to kisan nan fa tamkar bashi ka ɗauka, ko bajima ko ba dade zai dawo domin amsar biyan bashin sa.

El-rufai yayi wannan zancen ne a yayin da yake halartar wani taro a ranar Alhamis da “Africa Leadership Group” suka shirya ta kafar sadarwar nesa-da-nesa (Zoom), wanda jaridar “The Punch” suka ruwaito.


To sai dai kalaman na gwamnan basuyiwa mutane da yawa daɗi ba, musamman yan kudu, inda suka zargi cewar, ai daman abin baizo musu da mamaki ba , inda a cewar su suka ce ai daman an san sa da nuna wariya.

El-Rufai

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *