Kawo yanzu Fiya da Manya manyan gine ginen alfarma 20 Na Gwamnatin ne Suka kone~Minista Sadiya

Fiye da gine-ginen gwamnati da na masu zaman kansu 20 Suka kone kurmus a wannan shekarar, Gwamnatin Tarayya ta ce a ranar Juma’a. Ministan Harkokin Jin Kai da gudanar da Bala’i da Ci Gaban Jama’a, Sadiya Farouq, ta bayyana hakan a yayin da ma’aikatarta ta gudanar da wani atisayen Mai taken fita daga wuta a Sakatariyar Tarayya, Kashi na 1, Abuja, don tunawa da ranar 2020 ta Duniya na Rage Rashin Bala’i. Farouq ta ce makasudin atisayen fitar wuta / fitarwa shi ne tabbatar da domin tabbatar da Al’umma Cikin aminci da gujewa faruwar gobara.

Ta lura cewa irin wadannan atisayen zasu tabbatar da hana fargaba wanda ya kasance sanadiyyar asaran rayukan mutane a cikin manyan masifu na gobara. Ministan ta ce, “Abin da muka yi yanzu abin birgewa ne, la’akari da jerin abubuwan da bala’o’in gobara ke haddasawa a gine-ginen gwamnati da masu zaman kansu a Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published.