Labarai

Kishin Ƙasa: Yadda Wani Ɗan China ya Yankarwa Kansa Tikitin Gidan Cin Gabza a Najeriya Bayan Yayi wa Kuɗin Najeriya Yaga-Yaga.

Spread the love

Wani Alƙali Mai Suna Nicholas Oweibo dake Babbar Kotun Gwamnatin Tarayya dame Ikoy ta Jihar Legas ta ɗaure wani Ɗan Ƙasar China na tsawon Shekara biyu bayan ya yagalgala takardar Naira Dubu Ɗaya.

Lamarin dai ya faru ne a 17 ga watan Mayu na wannan shekarar, inda mutum ɗan Chana Ya zaro Naira Dubu Ɗaya cikin gadara, inda nan take ya kekketa ta a nan filin tashin sauka da tashin jiragen Murtala Muhammad dake Legas.

Shi dai mutumin sunansa Li Lei Lei. Kuma Hukumar kula da laifukan tattalin arziki da kuɗi ta Najeriya wato (EFCC) ta kamashi, inda takaishi kotu tace ya saɓawa dokar babban bankin Najeriya.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button