Labarai

Ko da ace ban tsaya takara ba to tabbas ba zan zabi Atiku da Obi ba domin basu da kwarewa da Chancantar aiki ~Cewar Bola Tinubu.

Spread the love

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Ahmed Tinubu, ya ce ba zai zabi daya daga cikin takwarorinsa na jam’iyyar PDP ko Labour Party (LP) ba idan da ace ba zai tsaya takara a 2023 ba.

Tsohon gwamnan na Legas ya bayyana matsayinsa ne a wata hira da BBC a ranar Litinin jim kadan bayan ya yi jawabi a gidan talabijin na Chatham da ke birnin Landan na kasar Birtaniya.

Da yake amsa tambaya kan ko zai zabi Atiku ko Obi idan ba ya takara, Tinubu ya ce, a.a domin ba su da kwarewa kamar sauran mutane a wajen. Ba su da wani tarihi, babu wanda ya cancanta a cikinsu sai ni.”

Tinubu ya kuma ce masu sukar tushen arzikinsa hassada ce ke sa hakan, yana mai cewa arzikinsa ya fito ne daga hannun jarin da ya samu.

Kuma shi ba ya rabon albarkatun Legas da gwamnatin jihar.

“Ba ina musun dukiyata ba. Ni ne aka fi bincike ni, gwamnan da aka fi tuhuma a jam’iyyar adawa na tsawon shekaru takwas, kuma tun da na bar ofis, ban dauki wani mukamin nadin gwamnati ko kwangilar gwamnati,” in ji shi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button