Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci tsohon shugaban kungiyar Shugaban Kasa na Gyaran Fansho (PPRTT), Abdulrasheed Maina ta bashi dama ya kare kansa a ranar 26 zuwa 27 ga watan Janairu.
Jastis Okon Abang a ranar Litinin ya bayyana cewa Maina na iya kiran shaidu kimanin 21, kamar yadda aka riga aka nuna a cikin ayyukansa, don bayar da shaida a madadinsa.
Lauyan Maina, Anayo Adibe a baya ya nemi izini don kawo kara da ke kalubalantar shari’ar a gaban kotu.
Amma Mai Shari’a Abang ya bayyana ‘yancinsa na ka Kare kansa. A cewar alkalin, bayan tsallake beli a yayin shari’ar, Maina ya sa kotun ta yanke hukuncin cewa za a ci gaba da shari’arsa ba tare da shi ba, ya kara da cewa ba a kalubalanci umarnin ba.
An gurfanar da Maina a ranar 25 ga Oktoba, 2019 a kan tuhume-tuhume 12 tare da dansa, Faisal kan tuhume-tuhume uku da suka hada da halatta kudaden haram, da boye kudaden da aka aikata ba bisa doka ba.
Daga karshe an sake shi a watan Yuni kan kudin belin N500 miliyan ko kuma wata kadara a Asokoro tare da Sanata Ndume a matsayin wanda zai tsaya masa.
Amma bayan ya gudu daga shari’ar, an tura dan majalisar a gidan kurkukun Kuje.
Amma, jami’an tsaro sun gabatar da Maina a kotu a ranar 4 ga Disamba, bayan da aka kama shi a makwabciyar Jamhuriyar Nijar kuma aka tasa keyarsa zuwa Najeriya.