Labarai

Kotu ta dakatar da yunkurin tilasta wa shugaban INEC murabus

Spread the love

Hukuncin na ranar Laraba ya kuma hana hukumar tsaro ta farin kaya, ‘yan sandan Najeriya da kuma hukumar da’ar ma’aikata (CCB) gudanar da bincike kan Mista Mahmood kan bayyana kadarorin sa.

A ranar Talata ne babbar kotun tarayya dake birnin Garki da ke babban birnin tarayya Abuja ta haramtawa jami’an tsaro cafke shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Yakubu Mahmood bisa zargin bayyana kadarorinsa na karya.

Mai shari’a Maryam Hassan ta yi watsi da zarge-zargen da ake yi wa Mahmood.

Hukuncin na ranar Laraba ya kuma hana hukumar tsaro ta farin kaya, ‘yan sandan Najeriya da kuma hukumar da’ar ma’aikata (CCB) gudanar da bincike kan Mista Mahmood kan bayyana kadarorin sa.

Zarge-zargen da ake yi wa Shugaban Hukumar INEC ya samo asali ne daga sammacin da Somadina Uzoamaka ta kai wa Mista Mahmood da Babban Lauyan Tarayya (AGF).

Mai da’awar ya roki kotun da ta bayar da umarnin tilasta wa Shugaban INEC ya sauka daga mukaminsa, har zuwa lokacin da za a gudanar da bincike kan zargin da ake masa.

Sai dai Mista Mahmood ya gabatar da karar da kotu ta ga ya cancanta.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button