Kotu Ta Hana Ƙungiyar Kwadago Zan-zangar Rage Farashin Fetur Da Wutar Lantarki.

Mai shari’a Ibrahim Galadima na Kotun Masana’antu ta kasa, da ke Abuja, a ranar Alhamis, ya hana kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) da Trade Union Congress (TUC) ci gaba da shirinsu na yin zanga-zangar a duk fadin kasar a ranar 28 ga Satumba.

Alkalin ya bayar da umarnin ne yayin yanke hukunci a kan tsohon karar da wata kungiya, kungiyar Peace and Unity Ambassadors Association ta shigar.

Kungiyoyin kwadagon biyu sun yi barazanar fara zanga-zanga a duk fadin kasar da kuma daukar matakin rufe masana’antu a wani yunkuri na tilasta wa Gwamnatin Tarayya ta sauya karin farashin famfo na farashin man fetur da na wutar lantarki a kwanan nan.

Mai shari’a Galadima ya umarci kungiyoyin kwadagon da kungiyoyin da ke karkashin su da su dakatar da shirin har sai an saurari karar da kuma tabbatar da bukatar a kan sanarwar da mai nema ya gabatar.

Ya kuma ba da umarnin wucin gadi wanda ya hana kungiyoyin kwadago rudani, hanawa, diban kaya ko hana ma’aikata ko talakawan Najeriya shiga ofishinsu a ranar 28 ga Satumba ko kuma wata rana.

Leave a Reply

Your email address will not be published.