Labarai

Kotu ta yankewa Shahararren mai garkuwa da mutane Evans hukuncin daurin shekaru 21 a gidan yari

Spread the love

Kotun manyan laifuka ta jihar Legas da ke zama a Ikeja ta yanke hukuncin daurin shekaru 21 a gidan kaso ga wani mai garkuwa da mutane, Chukwudumeme Onwuamadike, wanda aka fi sani da Evans.

Mai shari’a Oluwatoyin Taiwo ta yankewa Evans da wanda ake tuhumarsa, Victor Aduba hukuncin daurin shekaru 21 a gidan yari bisa laifin yin garkuwa da wani Sylvanus Hafia.

Evans da wadanda ake tuhumar sun kasance a gaban kotun bisa laifuka hudu da suka hada da hada baki, garkuwa da mutane, da kuma mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.

An zarge su da hada baki tare da yin garkuwa da Sylvanus Ahanonu Hafia da misalin karfe 5:30 na yammacin ranar 23 ga watan Yuni 2014, a Kara Street, Amuwo Odofin a Legas kuma ana zargin su da kama Hafia tare da tsare Hafia tare da neman a biya su kudin fansa dala miliyan biyu.

Amma wadanda ake tuhumar sun ki amsa laifin da ake tuhumar su da su.

Zaman kotu na ranar litinin shine hukunci na biyu akan mai garkuwa da mutane.

A baya dai mai shari’a Hakeem Oshodi ya yanke masa hukuncin daurin rai da rai tare da wasu mutane biyu bisa samun su da laifin hada baki da kuma yin garkuwa da Manajan Daraktan Kamfanin Magunguna na Maydon Pharmaceuticals Limited, Donatus Dunu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button