Labarai

Kowa ya dauki makami ya kare Kansa da Kansa daga ‘yan bindiga ~Cewar Gwamna Kaura ga al’ummar jihar Bauchi.

Spread the love

Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya bukaci mazauna al’ummar da aka kai wa hari kwanan nan a karamar hukumar Alkaleri da su tashi su dauki makamai su kare kansu daga ‘yan bindigar.

Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Alhamis a fadar Hakimin Yelwan Duguri, Alh Adamu Mohammed Duguri a ziyarar da ya kai kauyen Rimi, Gwana da Yalwan Duguri domin jajantawa wadanda ‘yan bindiga suka kai wa hari.

Ya ce lamarin wani Abu ne da ba za a amince da ita ba” wanda dole ne a dakatar da shi ko ta yaya.

“An san ku maza ne, kada ku bari waɗannan miyagun abubuwa su mallake ku, su kare ƙasarku, ku kwato kanku. Ku tashi ku dauki makami ku kare kanku,” inji shi.

Da yake mayar da martani, Hakimin Yelwa Duguri, Alhaji Adamu Mohammed Duguri, ya ce mutane 20 ne aka kashe a kauyen Rimi a lokacin hare-haren kuma yunkurinsu na kaiwa Kafin Duguri ya ci tura yayin da mutanen kauyen suka tashi domin kare kauyen.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button