Labarai

Kungiyar Direbobi masu dakon man fetur ta shirya tafiya yajin aiki saboda zargin da suke yiwa ma’aikatar ayyuka na karkatar da Naira Biliyan 621 kudin gyaran titina guda 21 da NNPC ta dauki nauyi.

Spread the love

Kungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas ta Najeriya a ranar Lahadin da ta gabata ta bayyana goyon bayanta ga matakin da kungiyar direbobin tankar mai ta NUPENG ke shirin dauka na fara yajin aikin kwatsam.

NUPENG ta kuma dage cewa binciken da ta gudanar ya nuna cewa a halin yanzu jami’an ma’aikatar ayyuka da gidaje ta tarayya suna karkatar da Naira biliyan 621 da kamfanin man fetur na Najeriya ya bayar domin gyaran manyan tituna guda 21.

Ko da yake ma’aikatar ayyuka ta musanta zargin, kungiyar ta yi zargin cewa Hotunan gyaran titunan da FMWH ta dauka, hotuna ne da aka dauka kafin a amince da N621bn.

Sun bayyana hakan ne a wata sanarwa da shugaban kungiyar Williams Akporeha da babban sakataren kungiyar, Olawale Afolabi suka sanyawa hannu, inda suka kara da cewa yarjejeniyar da aka cimma kan lamarin da gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki a tarurruka biyu daban-daban ba a kiyaye ba.

Sanarwar ta kara da cewa, “Wadannan tarurruka guda biyu sun sanya hannu kan wata takardar sanarwa da ke nuna shirye-shiryen da kuma niyyar kamfanin na NNPC na samar da kudaden gyara wasu muhimman tituna guda 21 a kan kudi N621bn ta hanyar tsarin biyan harajin ababen more rayuwa.

“Abin takaici, fargabar da muke da ita game da fafutukar ne sannu a hankali ke ta kunno kai tare da samun bayanai daga majiya mai tushe cewa wasu daga cikin gwamnatin Jihohi da jami’an ma’aikatar ayyuka da gidaje da kuma ‘yan siyasa masu ra’ayin rikau sun riga sun tsoma hannunsu cikin wadannan kudade sun karkatar da su zuwa hanyoyin da aka riga aka tsara kuma aka yi su tun shekarar da ta gabata.”

NUPENG ta kara da cewa, “Jami’an ma’aikatar ayyuka da gidaje suna zagayawa suna nuna hotunan titunan da aka yi a watan Yuni da Agusta 2021 don tabbatar da aikin na N621bn da aka amince da su a watan Oktoba 2021 na gyaran muhimman hanyoyi 21.

“Muna da hujjojinmu da alkalumman mu, kuma ba za mu bari N621bn ta tafi kamar yadda sauran kudaden da aka kasafta suka tafi ba.”

Kungiyar ta bukaci da a dakatar da ci gaba da fitar da asusun nan take har sai an kafa wata tawagar masu sa ido da tabbatar da cewa ta kunshi dukkan masu ruwa da tsaki da suka sanya hannu kan takardar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button