Labarai

Kungiyar Yarabawan jihar Kaduna sunce sun aminta Sanata Uba sani ya zama Gwamnan jihar Kaduna.

Spread the love

Kungiyar Yarabawa a jihar Kaduna sun goyi bayan takarar Sanata Uba sani amatsayin Gwamnan jihar Kaduna Sanatan ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook Yana Mai cewa Na yi matukar nuna ladabi da kai dangane da gagarumin goyon bayan da kungiyar Yarabawa ta Jihar Kaduna na neman zama gwamna, tare da ba ni lambar yabo ta girmamawa don ganin irin nasarorin da na samu a Majalisar Dokoki ta kasa. Hakan ya faru ne a yayin bikin ranar al’adun Yarabawa na majalisar 2022 wanda aka gudanar a dakin motsa jiki na Ahmadu Bello Stadium dake jihar Kaduna.

Yayin da nake nuna matukar godiyata, na ba su tabbacin cewa zan tafiyar da gwamnati dunkulalliya jiha da kasa ba tare da la’akari da kabila ko jinsi ba Na roke su da ka da su jajirce wajen goyon bayan takara na kawai ba face su ha’da da, na Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da dukkan ‘yan takarar babbar jam’iyyar mu ta APC a jihar Kaduna.

Sanata Uba sani shine Sanatan Kaduna ta tsakiya Kuma Dan takarar Gwamnan jihar Kaduna karkashin jam’iyar APC Wanda yanzu Haka yake samun karbuwa a Fuskokin al’ummar jihar ta Kaduna.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button