Shekaru da yawa da suka gabata bayan fitowar waya, yankin ja’en ya kasance wani wuri da yake fuskantar matsalar sace-sacen waya kamar sauran yankuna da sukai kaurin suna a Kano. Wannan yasa barayin tare duk wani mai tsautsayi ta hanyar kwace wayarsa da zarar wayar da zarar sun samu dama.
Hakan shine dalilin da yasa mutanen yankin suka yi ta maza suka dauki wani kwararren kwamandan yan vigilante (dan kato da gora) domin hana wadannan barayi cin Karen su babu babbaka. Haka kuwa akayi.

Wannan mutumin mai suna Abdulsalami Kamfa, yayi kaurin suna wajen kama masu satar waya tare da ganin ya hada su da jami’an tsaro domin fuskantar abinda suka shuka.
To amma wannan nadin da akayi masa, yazo ya tafi yabar baya da kura, domin kuwa awa daya da soma aikinsa keda wuya, watau bai dade da gama jawabin soma aikin saba, wasu mutane da ba’a san ko su waye ba suka sace masa wayar mai dan karen kyau da tsada nan take.

Kamar yadda Abdulsalami Kamfa ya shaidawa majiyar jaridar Mikiya (BBC PIDGIN), yayi amanna da cewa, wannan wata shaida ce da take nuna cewar yana da babban aiki a gabansa a wannan sabon mukami nasa da ya soma.
Rahoto: Abubakar Mustapha kiru