Labarai

kwankwaso babban shugaba ne a Nageriya ba zamuyi Wasa ba dole mu zauna dashi a Lokacin daya dace ~Cewar kashim Shettima.

Spread the love

Mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Sanata Kashim Shettima, ya ce shi da kan sa zai tuntubi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Dr Rabi’u Musa Kwankwaso a daidai lokacin da ya dace kafin zaben 2023.

Shettima wanda ke gabatar da lacca a taron limamai na babban birnin tarayya Abuja a jiya a Abuja a matsayin daya daga cikin bakin da aka gayyata, bisa ga dukkan alamu yana tafka barkwanci da wani tsohon dan majalisar wakilai Garba Ibrahim Muhammed wanda ya wakilci Sanata Kwankwaso a wajen taron. taron.

“Na sha alwashin ba zan yi maganar cin mutuncin Sanata Rabiu Kwankwaso ba a duk lokacin zabe mai zuwa. Babban shugaba ne, kuma in sha Allahu zamu zauna tare mu fahimci juna nan ba da jimawa ba.

“Wadanda ke shirin raba kasar nan ba za su yi nasara ba, don haka dole ne mu jure wa junanmu da sadaukarwa,” in ji Shettima.

Tun da farko a nasa jawabin shugaban kwamitin kungiyar Imam Tajuddeen Bello, ya ce taron ya samu halartar wakilan limamai daga dukkan jihohin kudancin kasar nan 17, mai taken: “Hadin kai na Imamai don Ci gaban kasa.”

Ya ce an kuma shirya irin wannan taro ga limaman jihohin Arewa 19 a bara.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button