Labari Mai dadi ga ‘yan kasuwa Buhari Zai Fara Bawa ‘yan kasuwa dubu N50,000 ko wanne wata

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Litinin, ya sanar da cewa, gwamnatin sa ta shirya kaddamar da wata gidauniyar tallafawa matsakaitu da kananan ‘yan kasuwa a Nigeria.

A wannan sabon shirin, a cewar shugaba Buhari, gwamnati za ta dinga tallafawa ‘yan kasuwar ne da N50,000 a kowanne wata.

Sai dai, gwamnati za ta dauki tsauraran matakai wajen zakulo ‘yan kasuwan da za su ci moriyar wannan tallafi, kuma ‘yan kasuwar za su fito daga kowanne fanni na kasuwanci.

Haka zalika, shugaban kasar ya ce a yunkurin gwamnatinsa na farfado da tattalin arziki, a farkon shekarar 2020, babban bankin Nigeria ya fitar da N100bn don tallafawa masana’antu.

A cikin N100bn na tallafin, an rabawa kamfanonin kiwon lafiya da sarrafa magunguna, wanda tuni aka kaddamar da shirye shirye 37, akan kudi N37bn.

Haka zalika, babban bankin ya fitar da tiriliyan daya, don tallafawa bangaren masana’antun kere kere, inda tuni aka raba N191bn daga cikin kudin.

Haka zalika, babban bankin ya fitar da tiriliyan daya, don tallafawa bangaren masana’antun kere kere, inda tuni aka raba N191bn daga cikin kudin.

Mai tallafawa shugaban kasar ta fuskar kafofin sadarwa na zamani, Mr Tolu Ogunlesi ne ya fitar da sanarwar a shafinsa na Twitter.

Leave a Reply

Your email address will not be published.