LABARIN SA: Jami’an hukumar Costom ne sukayi masa haka

Wannan Bawan allah daga Garin Daddara ta karamar hukumar jibyan jihar katsina ya dakko buhun sikari Sugar akan babur dinsa zai Shiga Cikin garin katsina Su Kuma Jami’an hukumar kwaston suna tafiya a hanya suka ganshi shine Suka sa motarsu suka bugeshi shi da babur din nasa Bayan sun makeshi suka dauke buhun sikarin suka wuce dashi sa’an nan suka barshi kwance cikin jini sunyi zaton ya mutu ne wasu bayin Allah ne suka same shi Cikin jini suka daukeshi a Kan hanya Bayan ya farfado anyi Masa tambya Amma kafin ya bayarda amsa sai kuka yake…

Daga karshe shine yayi bayanin Abinda Jami’an hukumar kwaston din sukayi masa, daaga Jamilu Ali Radi

Leave a Reply

Your email address will not be published.