Lallai gobe sabar Ku Fara duban watan sh’aban Sakon Sultan Zuwa musilman Nageriya.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar III ya umarci al’ummar Musulmi cewa Lallai su Fara neman sabon watan Sha’aban 1442AH daga gobe ranar Asabar.

Mista Abubakar ya yi wannan kiran ne a ranar Juma’a a cikin wata sanarwa da Farfesa Sambo Junaidu, Shugaban Kwamitin Ba da Shawara Kan Harkokin Addini, Majalisar Masarautar Sakkwato.

Wannan itace sanarwa ga al’ummar musulmi cewa ranar Asabar 13 ga Maris, wacce tayi daidai da 29 ga watan Rajab 1442AH zata kasance ranar Farko ta neman sabon watan Sha’aban 1442AH.

“Don haka aka bukaci Musulmai dasu fara neman sabon wata a ranar Asabar kuma Duk Wanda ya gani ya kai rahoton ganin sa zuwa Gundumar da ke kusa ko Shugaban Kauyen don ci gaba da sadarwa ga Sarkin Musulmi,’ in ji shi.

Sarkin Musulmin ya roki Allah da ya taimaka wa Musulmai wajen sauke nauyin da ke kan su na addini.

Sha’aban shi ne wata na takwas a kalandar Musulunci, wanda ke zuwa kafin azumin watan azumin Ramadan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *